Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 36:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A sa'ad da Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, yana shekara huɗu da sarauta, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

2. “Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra'ila, da Yahuza, da dukan al'ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau.

3. Mai yiwuwa ne idan mutanen Yahuza suka ji dukan masifar da na yi niyya in aukar musu da ita, za su bar mugayen ayyukansu don in gafarta musu muguntarsu da zunubinsu.”

4. Sai Irmiya ya kirawo Baruk ɗan Neriya. Baruk kuwa ya rubuta maganar da Irmiya ya faɗa masa a takarda, wato dukan maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya.

5. Sai Irmiya ya umarci Baruk, ya ce, “An hana ni zuwa Haikali,

6. saboda haka kai za ka tafi. A ranar azumi za ka karanta wa mutane maganar Ubangiji, wadda take a takardar da ka rubuta ta wurin shibtar da na yi maka. Ka karanta ta a cikin Haikali, a gaban mutanen Yahuza waɗanda suka fito daga biranensu.

7. Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.”

8. Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya umarce shi. Ya karanta takardan nan ta maganar Ubangiji a Haikalin Ubangiji.

9. A watan tara a shekara ta biyar ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, sai dukan jama'ar Urushalima da dukan jama'ar da suka zo Urushalima daga biranen Yahuza suka yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji.

10. Sai Baruk ya karanta maganar Irmiya wadda take a takardar, kowa yana ji, a cikin Haikali a ɗakin Gemariya ɗan Shafan, magatakarda. Ɗakinsa yana a shirayi na bisa a hanyar shiga Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11. Sa'ad da Mikaiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji da take a littafin,

12. sai ya gangara gidan sarki, ya shiga ɗakin magatakarda, inda dukan shugabanni suke zaune, wato Elishama magatakarda, da Delaiya ɗan Shemaiya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemariya ɗan Shafan, da Zadakiya ɗan Hananiya, da dukan sarakuna.

13. Sai Mikaiya ya faɗa musu dukan maganar da ya ji sa'ad da Baruk ya karanta littafin a kunnuwan jama'a.

14. Sai dukan sarakunan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya faɗa wa Baruk ya kawo littafin nan da ya karanta wa jama'a. Sai Baruk ɗan Neriya ya ɗauki littafin ya je wurinsu.

15. Suka ce masa ya zauna, ya karanta musu littafin. Baruk kuwa ya karanta musu.

Karanta cikakken babi Irm 36