Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 34:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

13. “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari da kakanninku lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar daga bauta, na ce,

14. ‘A shekara ta bakwai, dole ne ku 'yantar da 'yan'uwanku, Ibraniyawa, waɗanda aka sayar muku, suka kuwa bauta muku shekara shida. Dole ne ku 'yantar da su daga bautarku.’ Amma kakanninku ba su kasa kunne gare ni ba.

15. A 'yan kwanakin da suka wuce kuka yi abu mai kyau a gabana da kuka tuba, har kuka yi wa juna shelar 'yanci. Kuka yi alkawari a gabana a Haikalin da ake kira da sunana.

16. Amma sai kuka sāke tunaninku, kuka ɓata sunana sa'ad da kowannenku ya komo da bayinsa, mata da maza, waɗanda kuka 'yantar, don su zauna yadda suke so. Ga shi kuma, kun komo da su su zama bayinku.

17. Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.

18. Mutanen da suka keta alkawarina, ba su kuma kiyaye maganar alkawarin da suka yi a gabana ba, sa'ad da suka raba ɗan maraƙi kashi biyu, suka bi ta tsakiyarsa,

19. wato manyan fādawan Yahuza, da na Urushalima, da 'yan majalisa, da firistoci da dukan jama'ar ƙasa, waɗanda suka bi ta tsakanin rababben ɗan maraƙin,

20. zan bashe su a hannun abokan gabansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsaye da namomin jeji.

21. Zadakiya, Sarkin Yahuza kuwa, da sarakunansa, zan bashe su a hannun abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, wato sojojin Sarkin Babila, waɗanda suka tashi suka bar ku.

22. Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”

Karanta cikakken babi Irm 34