Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 32:18-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.

19. Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.

20. Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.

21. Ta wurin alamu da al'ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama'arka Isra'ila daga ƙasar Masar.

22. Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka.

23. Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.

24. “Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.

Karanta cikakken babi Irm 32