Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 2:4-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila.

5. Ubangiji ya ce,“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,Da suka bar bina?Suka bauta wa gumaka marasaamfani,Su kuma suka zama marasa amfani.

6. Ba su kula da ni ba,Ko da yake na cece su daga ƙasarMasar.Na bi da su a cikin hamada,A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,Busasshiya mai yawan hatsari,Ba a bi ta cikinta,Ba wanda yake zama cikinta kuma.

7. Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi,Don su more ta su ci amfaninta,Amma da suka shiga, sun ƙazantarmini da ita,Suka sa ƙasar da na gādar musu tazama abar ƙyama.

8. Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina UbangijiYake?’ ba.Masanan shari'a ba su san ni ba.Masu mulki sun yi mini laifi,Annabawa sun yi annabci da sunanBa'al,Sun bi waɗansu abubuwa marasaamfani.”

9. “Domin haka, ni Ubangiji zangabatar da ku gaban shari'a,Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan'ya'yanku, wato jikokinku.

10. Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajenyamma, ku gani,Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, kuduba da kyau,A dā an taɓa yin wani abu haka?

11. Akwai wata al'umma da ta taɓasāke gumakantaKo da yake su ba kome ba ne?Amma mutanena sun sauya darajarsuda abin da ba shi da rai.

12. Sammai, ku girgiza saboda wannan,ku razana,Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.

13. Mutanena sun yi zunubi iri biyu,Sun rabu da ni, ni da nakemaɓuɓɓugar ruwan rai,Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa,hudaddu,Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.

14. “Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kumahaife shi bawa ba,Amma me ya sa ya zama ganima?

15. Zakuna suna ruri a kansa,Suna ruri da babbar murya.Sun lalatar da ƙasarsa,Garuruwansa sun lalace,Ba wanda yake zaune cikinsu.

16. Mutanen Memfis kuma da naTafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.

17. Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kankawannan,Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,Sa'ad da ya bishe ka a hanya.

18. Wace riba ka samu, har da ka tafiMasar,Don ka sha ruwan Kogin Nilu?Wace riba ka samu, har da ka tafiAssuriya,Don ka sha ruwan KoginYufiretis?

19. Muguntarka za ta hore ka,Riddarka kuma za ta hukunta ka.Sa'an nan za ka sani, ka kumagane,Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a garekaKa rabu da Ubangiji Allahnka,Ba ka tsorona a zuciyarka.Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna nafaɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 2