Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 2:25-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunkaba takalma,Kada kuma ka bar maƙogwaronkaya bushe.Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwazan bi.’

26. “Kamar yadda ɓarawo yakan shakunya sa'ad da aka kama shi,Haka nan mutanen Isra'ila za su shakunya,Da su, da sarakunansu, dashugabanninsu,Da firistocinsu, da annabawansu.

27. Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai nemahaifinmu.’Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, kahaife mu.’Gama sun ba ni baya, ba su fuskanceni ba.Amma sa'ad da suke shan wahala,sukan ce,‘Ka zo ka taimake mu.’

28. Ina gumakan da kuka yi wakanku?Bari su tashi in sun iya cetonkulokacin wahalarku.Yahuza, yawan gumakanku sun kaiYawan garuruwanku.

29. Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Waceƙara kuke da ita game da ni?’Kun yi mini tawaye dukanku.

30. Na hori 'ya'yanku, amma a banza, basu horu ba,Kun kashe annabawanku da takobikamar mayunwacin zaki.

Karanta cikakken babi Irm 2