Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 2:14-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. “Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kumahaife shi bawa ba,Amma me ya sa ya zama ganima?

15. Zakuna suna ruri a kansa,Suna ruri da babbar murya.Sun lalatar da ƙasarsa,Garuruwansa sun lalace,Ba wanda yake zaune cikinsu.

16. Mutanen Memfis kuma da naTafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.

17. Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kankawannan,Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,Sa'ad da ya bishe ka a hanya.

18. Wace riba ka samu, har da ka tafiMasar,Don ka sha ruwan Kogin Nilu?Wace riba ka samu, har da ka tafiAssuriya,Don ka sha ruwan KoginYufiretis?

19. Muguntarka za ta hore ka,Riddarka kuma za ta hukunta ka.Sa'an nan za ka sani, ka kumagane,Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a garekaKa rabu da Ubangiji Allahnka,Ba ka tsorona a zuciyarka.Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna nafaɗa.”

20. “Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙiyardaUbangiji ya mallake ka,Ka ƙi yin biyayya da ni,Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’Amma ka yi karuwanci a kankowane tudu,Da kowane ɗanyen itace.

21. Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyarkurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafikyau.Ta yaya ka lalace haka ka zamarassan kurangar inabi ta jeji,Waɗanda ba zan yarda da su ba?

22. Ko da za ka yi wanka da sabulunsalo,Ka yi amfani da sabulu mai yawa,Duk da haka zan ga tabbanzunubanka.Ni Ubangiji Allah na faɗa.

23. Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar dakanka ba,Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba?Ka duba hanyarka ta zuwa cikinkwari, ka san abin da ka yi.Kana kama da taguwa, mai yawonneman barbara.

24. Kamar jakar jeji kake, wadda takeson barbara,Wadda take busar iska,Sa'ad da take son barbara, wa zai iyahana ta?Jakin da take sonta, ba ya bukatarwahalar da kansaGama a watan barbararta za a sameta.

25. Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunkaba takalma,Kada kuma ka bar maƙogwaronkaya bushe.Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwazan bi.’

26. “Kamar yadda ɓarawo yakan shakunya sa'ad da aka kama shi,Haka nan mutanen Isra'ila za su shakunya,Da su, da sarakunansu, dashugabanninsu,Da firistocinsu, da annabawansu.

27. Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai nemahaifinmu.’Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, kahaife mu.’Gama sun ba ni baya, ba su fuskanceni ba.Amma sa'ad da suke shan wahala,sukan ce,‘Ka zo ka taimake mu.’

Karanta cikakken babi Irm 2