Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 17:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce, “An rubuta zunubin mutanen Yahuza da alƙalamin ƙarfe, mai bakin yakutu. An zana shi a allon zuciyarsu da a zankayen bagadansu.

2. Idan sun tuna da 'ya'yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi.

3. Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar.

4. Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”

5. Ubangiji ya ce,“La'ananne ne mutumin da yakedogara ga mutum,Wanda jiki ne makaminsa,Wanda ya juya wa Ubangiji baya,

6. Gama yana kama da sagagi ahamada,Ba zai ga wani abu mai kyau yanazuwa ba.Zai zauna a busassun wurarenhamada,A ƙasar gishiri, inda ba kowa.

7. “Mai albarka ne mutumin da yakedogara ga Ubangiji,Wanda Ubangiji ne madogararsa.

8. Shi kamar itace ne wanda ake dasa abakin rafiWanda yake miƙa saiwoyinsa zuwacikin rafin,Ba zai ji tsoron rani ba,Kullum ganyensa kore ne,Ba zai damu a lokacin fari ba,Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.

9. “Zuciya ta fi kome rikici,Cuta gare ta matuƙa,Wa zai san kanta?

10. Ni Ubangiji nakan bincike tunani,In gwada zuciya,Domin in sāka wa kowane mutumgwargwadon al'amuransa,Da kuma gwargwadon ayyukansa.

Karanta cikakken babi Irm 17