Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 16:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ba za ka yi aure ka haifi 'ya'ya mata da maza a wannan wuri ba.

3. Ga abin da ni Ubangiji na faɗa a kan 'ya'ya mata da maza da aka haifa a wannan wuri, da kuma a kan iyayensu mata da maza da suka haife su a wannan ƙasa,

4. za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”

5. Ubangiji kuma ya ce, “Kada ka shiga gidan da ake makoki, ko ka tafi inda ake baƙin ciki, kada ka yi baƙin ciki saboda su, gama na ɗauke salamata, da ƙaunata, da jinƙaina daga wurin jama'an nan.

6. Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu.

Karanta cikakken babi Irm 16