Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 15:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.

5. “Wa zai ji tausayinki, yaUrushalima?Wa zai yi baƙin ciki dominki?Wa kuma zai ratso wurinki don yatambayi lafiyarki?

6. Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna takomawa da baya,Don haka na nuna ikona gāba da ku,na hallaka ku,Na gaji da jin tausayinku!

7. Na sheƙe su da abin sheƙewa aƙofofin garuruwan ƙasar.Na sa 'ya'yansu su mutu, na hallakamutanena,Ba su daina yin mugayen ayyukansuba.

Karanta cikakken babi Irm 15