Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 11:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya cewa,

2. “Ka ji maganar wannan alkawari, sa'an nan ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima.

3. Ka faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, la'ananne ne wanda bai kula da maganar alkawarin nan ba.

4. Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu.

5. Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ”Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”

6. Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuza da titunan Urushalima duka, cewa su ji maganar alkawarin nan, su aikata.

7. Lokacin da na fito da kakanninsu daga ƙasar Masar na faɗakar da su musamman, na yi ta faɗakar da su har wannan rana, ina cewa, ‘Ku yi biyayya da maganata.’

8. Amma duk da haka ba su yi biyayya ba, ba su kuma kasa kunne ba. Kowa ya bi tattaurar zuciyarsa mai mugunta. Domin haka na kawo musu dukan maganar alkawarin nan wanda na umarce su su yi, amma ba su yi ba.”

9. Ubangiji ya kuma ce mini, “Akwai tawaye a cikin mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima.

Karanta cikakken babi Irm 11