Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 1:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. “Na san ka tun kafin a yi cikinka,Na keɓe ka tun kafin a haife ka,Na sa ka ka zama annabi gaal'ummai.”

6. Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah!Ban san abin da zan faɗa ba,Gama ni yaro ne.”

7. Amma Ubangiji ya ce mini,“Kada ka ce kai yaro ne,Kai dai ka tafi wurin mutanen da zanaike ka,

8. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare dakai,Zan kiyaye ka.Ni Ubangiji na faɗa.”

9. Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini,“Ga shi, na sa maganata a bakinka.

10. Ga shi, a wannan rana na ba ka iko akan al'ummai da mulkoki,Don ka tumɓuke, ka rusar,Ka hallakar, ka kaɓantar,Ka gina, ka dasa.”

11. Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?”Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”

12. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”

13. Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Me kuma ka gani?”Na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, daga wajen arewa kamar za ta jirkice wajen kudu.”

14. Sai Ubangiji ya ce mini, “Daga wajen arewa masifa za ta fito ta auka wa dukan mazaunan ƙasar.

Karanta cikakken babi Irm 1