Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 1:15-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ga shi kuwa, ina kiran dukan kabilan mulkokin arewa, za su kuwa zo su kafa gadajen sarautarsu a ƙofofin Urushalima, su kewaye dukan garukanta da dukan sauran biranen Yahuza.

16. Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi.

17. Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu.

18. Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.

19. Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 1