Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Hab 3:13-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ka fito saboda ceton mutanenka,Saboda ceton shafaffenka kuma.Ka fasa kan mugu,Ka kware shi daga cinya zuwa wuya.

14. Ka kuje kan mayaƙansa da sandunansa,Waɗanda suka zo kamar guguwa don su watsar da mu.Suna murna kamar waɗanda suke zaluntar matalauci a ɓoye.

15. Ka tattake teku da dawakanka,Da haukan ruwa mai ƙarfi.

16. Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa,Leɓunana suka raurawa.Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki.Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zoA kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.

17. Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba,Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi,Zaitun kuma bai ba da amfani ba,Gonaki ba su ba da abinci ba,An kuma raba garken tumaki daga cikin garke,Ba kuma shanu a turaku,

18. Duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,Zan yi murna da Allah Mai Cetona.

19. Ubangiji Allah shi ne ƙarfina,Ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi,Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.

Karanta cikakken babi Hab 3