Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Hab 1:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ba kai ne madawwami ba?Ya Ubangiji Allahna Mai Tsarki.Ba za mu mutu ba.Ya Ubangiji, kai ne ka sa su su yi hukunci,Ya dutse, kai ne ka kafa su don su yi horo.

13. Kai mai tsarki ne,Ka fi ƙarfin ka dubi mugunta.Kai da ba ka duban laifi.Me ya sa kake duban marasa imani?Kana iya shiru sa'ad da mugu yake haɗiyeMutumin da ya fi shi adalci?

14. Gama ka mai da mutane kamar kifaye a cikin teku,Kamar abubuwa masu rarrafe da ba su da shugaba.

15. Kaldiyawa sukan kama mutane da ƙugiya,Sukan jawo su waje da tarunsa,Sa'an nan su tara su cikin ragarsu,Su yi murna da farin ciki.

16. Domin haka sukan miƙa hadaya ga tarunsa,Su ƙona turare ga ragarsu,Domin su ne suka jawo musu wadata, da abinci mai yawa.

17. Za su ci gaba da juye tarunsa ke nan?Su yi ta karkashe al'umman duniya ba tausayi?

Karanta cikakken babi Hab 1