Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Hab 1:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Jawabin da annabi Habakuk ya hurta ke nan.

2. Ya Ubangiji, ina ta kukan neman taimako,Amma ka ƙi ji, sai yaushe za ka ji?Ina kuka a gare ka saboda zalunci,Amma ba ka yi taimako ba.

3. Me ya sa ka sa ni in ga mugunta,In kuma dubi wahala?Hallaka da zalunci suna a gabana.Jayayya da gardama sun tashi.

4. Ba a bin doka,Shari'a kuma ba ta aiki.Mugaye sun fi adalai yawa nesa,Don haka shari'a tana tafe a karkace.

Karanta cikakken babi Hab 1