Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 8:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin Fir'auna, ka ce masa, ‘Ubangiji ya ce ka saki jama'arsa domin su yi masa sujada.

2. Idan ka ƙi sakinsu, zai hore ka da kwaɗi.

3. Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama'arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka,

4. har ma za su hau bisa kanka, da jama'arka, da dukan fādawanka.’ ”

Karanta cikakken babi Fit 8