Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 6:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. 'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu.

18. 'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku.

19. 'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.

20. Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.

21. 'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri.

22. 'Ya'ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri.

23. Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

24. 'Ya'ya maza na Kora, su ne Assir, da Elkana, da Abiyasaf. Waɗannan su ne iyalin Kora.

25. Ele'azara, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Futiyel. Ita kuwa ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan kabilar Lawi bisa ga kabilansu.

Karanta cikakken babi Fit 6