Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 6:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, su tafi wurin Isra'ilawa da wurin Fir'auna, Sarkin Masar, su ba su umarni, su kuma fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar.

14. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu.

15. 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan Bakan'aniya, waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.

16. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. Lawi ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.

17. 'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu.

18. 'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku.

19. 'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.

20. Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.

21. 'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri.

22. 'Ya'ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri.

23. Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

Karanta cikakken babi Fit 6