Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 6:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”

2. Allah kuma ya yi magana da Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji.

3. Na bayyana ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a kan ni Allah Maɗaukaki ne, amma sunan nan nawa, Yahweh, ban sanasshe su ba.

4. Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci.

5. Yanzu na ji nishin Isra'ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina.

6. Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.

7. Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa.

8. Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.”’

9. Sai Musa ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta.

10. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

11. “Tafi gaban Fir'auna, Sarkin Masar, ka faɗa masa ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.”

Karanta cikakken babi Fit 6