Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 38:24-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

25. Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama'a talanti ɗari ne, da shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

26. Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550).

27. An mori azurfa talanti ɗari don yin kwasfa na alfarwa, da kwasfa na labule. An yi kwasfa ɗari da azurfa talanti ɗari, wato kwasfa ɗaya talanti ɗaya ke nan.

28. An yi maratayan dirkoki da azurfa shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775), sa'an nan an dalaye kawunansu, an kuma yi musu maɗaurai.

29. Tagullar da aka bayar kuwa, talanti saba'in da shekel dubu biyu da ɗari huɗu (2,400).

30. Da tagullar ce ya yi kwasfan ƙofar alfarwa ta sujada, da bagade, da ragarsa, da dukan kayayyakin bagaden.

Karanta cikakken babi Fit 38