Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 37:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwantar da murfin da fikafikansu. Fuskokinsu kuma na duban juna, suna kuma fuskantar murfin.

10. Sai kuma ya yi tebur da itacen ƙirya, tsawsonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

11. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya yi masa dajiya da zinariya.

12. Ya yi masa dajiya mai fāɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya kewaye da ita.

13. Ya yi wa tebur ɗin ƙawane huɗu na zinariya, ya manna ƙawane a kusurwoyi huɗu na ƙafafunsa.

14. Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin.

15. Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya.

16. Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.

17. Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin.

18. Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.

19. A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni.

20. A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni.

21. Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin.

Karanta cikakken babi Fit 37