Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 37:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

2. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye da shi.

3. Ya sa masa ƙawanya huɗu na zinariya a kan kusurwoyinsa huɗu, ƙawane biyu a wannan gefe, biyu kuma a wancan gefe.

4. Ya kuma yi sandunan da itacen ƙirya, ya dalaye su da zinariya.

5. Sai ya zura sandunan cikin ƙawanen da suke a gyaffan akwatin don ɗaukarsa.

6. Ya yi murfin da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

7. Ya kuma ƙera siffofin kerubobi biyu da zinariya, ya maƙala su a gefe biyu na murfin.

8. Kerub ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a wancan gefe. Ya yi su a haɗe da murfin a gefe biyu na murfin.

9. Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwantar da murfin da fikafikansu. Fuskokinsu kuma na duban juna, suna kuma fuskantar murfin.

10. Sai kuma ya yi tebur da itacen ƙirya, tsawsonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

11. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya yi masa dajiya da zinariya.

Karanta cikakken babi Fit 37