Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 36:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai dukan mutane masu gwaninta daga cikin ma'aikatan, suka yi alfarwa da labule goma. An yi labulen da lallausan zaren lilin na shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

9. Tsawon kowane labule kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Dukan labulen girmansu ɗaya ne.

10. Ya ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, haka kuma ya yi da sauran labule biyar.

11. Sai ya sa shuɗɗan hantuna a karbun labule na fari da na biyu.

12. Ya sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Dukan hantunan suna daura da juna.

13. Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labule da juna da maɗauran domin alfarwa ta zama ɗaya.

14. Ya kuma yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki domin ya rufe alfarwa.

15. Tsawon kowane labule kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Labule goma sha ɗayan nan girmansu ɗaya ne.

16. Ya harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, shida kuma ya harhaɗa su wuri ɗaya.

17. Sai ya yi hantuna hamsin, ya sa a karbu na bisa na labule na farin, haka kuma ya sa hantuna hamsin a karbun sama na labule na biyu.

18. Ya kuma yi maɗaurai da tagulla waɗanda zai harhaɗa hantuna da su don alfarwa ta zama ɗaya.

19. Ya yi wa alfarwa murfi da fatun raguna da aka rina ja, ya kuma yi wani abin rufewa da fatuna da aka jeme.

20. Ya kuma yi katakan alfarwa da itacen ƙirya.

Karanta cikakken babi Fit 36