Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 36:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Gama abin da aka kawo ya isa yin aikin, har da ragi.

8. Sai dukan mutane masu gwaninta daga cikin ma'aikatan, suka yi alfarwa da labule goma. An yi labulen da lallausan zaren lilin na shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

9. Tsawon kowane labule kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Dukan labulen girmansu ɗaya ne.

10. Ya ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, haka kuma ya yi da sauran labule biyar.

11. Sai ya sa shuɗɗan hantuna a karbun labule na fari da na biyu.

12. Ya sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Dukan hantunan suna daura da juna.

13. Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labule da juna da maɗauran domin alfarwa ta zama ɗaya.

14. Ya kuma yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki domin ya rufe alfarwa.

Karanta cikakken babi Fit 36