Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 36:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Da Bezalel da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima, waɗanda Ubangiji ya ba su hikima da basira na sanin yin kowane irin aiki, za su shirya Wuri Mai Tsarki kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

2. Sai Musa ya kirayi Bezalel, da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima wanda Ubangiji ya ba shi hikima a zuciya, da duk wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo, ya yi aikin.

3. Su kuwa suka karɓa daga wurin Musa dukan sadaka ta yardar rai da Isra'ilawa suka kawo don yin aikin alfarwa ta sujada. Jama'a suka yi ta kawo masa sadaka ta yardar rai kowace safiya.

4. Sai masu hikiman da suke yin aiki na alfarwa ta sujada suka ɗan dakatar da aiki suka tafi wurin Musa.

5. Suka ce masa, “Jama'a suna ta kawo sadaka fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.”

6. Sai Musa ya umarce su su yi shela a zango cewa, “Kada wata mace ko wani namiji ya sāke kawo sadaka don aikin alfarwa ta sujada.” Sai jama'a suka daina kawowa.

7. Gama abin da aka kawo ya isa yin aikin, har da ragi.

Karanta cikakken babi Fit 36