Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 35:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Musa kuma ya ce wa taron jama'ar Isra'ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta,

5. ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla,

6. da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin, da gashin awaki,

7. da fatun raguna da aka rina suka zama ja, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

8. da man fitila, da kayan yaji domin man keɓewa da turaren ƙonawa,

9. da duwatsu masu tamani, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.”

10. “Bari dukan wanda yake da fasaha a cikinku ya zo, ya yi aikin da Ubangiji ya umarta a yi,

11. wato aikin alfarwa ta sujada, da alfarwarta da murfinta, da maratayai, da katakanta da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

12. da akwati da sandunansa, da murfinsa, da labulen ƙofar.

13. Da tebur da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,

14. da alkuki don haske, da kayayyakinsa, da fitilunsa, da man fitila,

Karanta cikakken babi Fit 35