Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 35:14-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. da alkuki don haske, da kayayyakinsa, da fitilunsa, da man fitila,

15. da bagaden turaren ƙonawa da sandunansa, da man keɓewa mai ƙanshi, da turaren ƙonawa, da labulen ƙofar alfarwa ta sujada,

16. da bagaden ƙona hadaya da ragarsa ta tagulla da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da daro da gammonsa,

17. da labulen farfajiya da dirkokinsa da kwasfansu, da labulen ƙofar farfajiyar,

18. da turakun alfarwa, da turakun farfajiyar, da igiyoyinsu,

19. da saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a Wuri Mai Tsarki, da tsarkakakkun tufafin Haruna firist, da tufafin 'ya'yansa maza na aikin firist.”

20. Sa'an nan dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga wurin Musa.

21. Duk wanda ya yi niyya, da wanda ruhunsa ya iza shi ya kawo wa Ubangiji sadaka don yin alfarwa ta sujada, da dukan ayyukansa, da tsarkakakkun tufafi.

22. Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.

23. Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su.

24. Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi.

25. Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

26. Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki.

Karanta cikakken babi Fit 35