Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 35:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Musa ya tattara dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi.

2. Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi.

3. Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”

4. Musa kuma ya ce wa taron jama'ar Isra'ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta,

5. ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla,

6. da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin, da gashin awaki,

7. da fatun raguna da aka rina suka zama ja, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

8. da man fitila, da kayan yaji domin man keɓewa da turaren ƙonawa,

9. da duwatsu masu tamani, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.”

Karanta cikakken babi Fit 35