Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 31:16-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Domin wannan fa Isra'ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne.

17. Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra'ilawa, cewa a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da Ć™asa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta.”’

18. Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.

Karanta cikakken babi Fit 31