Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 31:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

2. “Ga shi, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.

3. Na cika shi da Ruhuna, da hikima, da basira, da ilimi, da fasaha,

4. don ya yi fasalin abubuwa na zinariya, da azurfa, da tagulla,

5. da yankan duwatsu masu tamani na jerawa, da sassaƙa itace, da kowane irin aikin fasaha.

6. Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka

7. a kan alfarwar ta sujada da akwatin alkawari, da murfin da yake bisansa, da dukan kayayyakin da yake cikin alfarwar,

8. da teburin da kayayyakinsa, da alkuki na zinariya tsantsa tare da dukan kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,

9. da bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa,

10. da saƙaƙƙun tufafi, wato da tsarkakakkun tufafin Haruna da na 'ya'yansa maza domin aikin firistoci,

Karanta cikakken babi Fit 31