Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 3:18-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’

19. Amma na sani Sarkin Masar ba zai bar ku ku fita ba, sai an yi masa tilas.

20. Domin haka zan miƙa hannuna in bugi Masar da dukan mu'ujizaina waɗanda zan aikata cikinta, sa'an nan zai bar ku ku fita.

21. “Zan sa wannan jama'a su yi farin jini a idanun Masarawa, sa'ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba.

22. Amma kowace mace za ta roƙi maƙwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa 'ya'yanku mata da maza. Da haka za ku washe Masarawa.”

Karanta cikakken babi Fit 3