Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 27:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da tagulla.

7. Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa.

8. Za ku yi bagaden da katakai, sa'an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.

9. “Za ku yi wa alfarwa farfajiya. A kudancin farfajiyar, sai ku rataye labule mai tsawo kamu ɗari wanda aka saƙa da lallausan zaren lilin.

10. Za ku yi masa dirkoki guda ashirin, da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

11. A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

12. Fāɗin labulen a wajen yamma na farfajiyar, zai zama kamu hamsin. A yi wa labulen dirkoki goma, a kuma yi wa dirkokin kwasfa goma.

13. Fāɗin labulen wajen gabas na farfajiyar zai zama kamu hamsin.

14. Labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

15. Haka kuma labulen ƙofa na wancan gefe zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

Karanta cikakken babi Fit 27