Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 27:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

12. Fāɗin labulen a wajen yamma na farfajiyar, zai zama kamu hamsin. A yi wa labulen dirkoki goma, a kuma yi wa dirkokin kwasfa goma.

13. Fāɗin labulen wajen gabas na farfajiyar zai zama kamu hamsin.

14. Labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

15. Haka kuma labulen ƙofa na wancan gefe zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

16. Za a saƙa labule mai kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai launi shuɗi, da shunayya, da mulufi domin ƙofar farfajiyar. Za a sa wa ƙofar dirkoki huɗu tare da kwasfansu huɗu.

17. Za a yi wa dukan dirkokin da suke kewaye da farfajiyar maɗaurai da maratayai na azurfa, da kwasfa ta tagulla.

18. Tsawon farfajiyar zai zama kamu ɗari, fāɗinta kamu hamsin, tsayinta kamu biyar. Za a saƙa labulenta da lallausan zaren lilin, a kuma yi kwasfanta da tagulla.

19. Da tagulla kuma za a yi turakun alfarwar, da turakun farfajiyar, da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a cikin alfarwar.”

Karanta cikakken babi Fit 27