Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 26:31-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. “Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa.

32. Ku rataye shi a bisa dirkoki huɗu nan itacen ƙirya waɗanda aka dalaye da zinariya, da maratayansu na zinariya waɗanda aka sa cikin kwasfa huɗu na azurfa.

33. Za ku sa labulen a ƙarƙashin maɗauran, sa'an nan ku shigar da akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba tsakanin Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki.

34. Ku sa murfin a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki.

35. Sai ku sa teburin a gaban labulen wajen arewa, ku kuma sa alkukin a kudancin alfarwar daura da teburin.

36. Haka nan kuma za ku yi wa ƙofar alfarwa makari da lallausan zaren lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi, aikin mai gwaninta.

37. Ku yi dirkoki biyar da itacen ƙirya saboda makarin, ku dalaye su da zinariya. Ku kuma yi maratayansu da zinariya. Ku yi wa waɗannan dirkoki kwasfa biyar da tagulla.”

Karanta cikakken babi Fit 26