Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 26:24-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwan nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu.

25. Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu.

26. “Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya.

27. Biyar kuma domin katakai na wancan gefe. Har yanzu kuma biyar domin katakai na gefen yamma.

28. Sandan da yake tsakiyar katakan zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe.

29. Za ku dalaye katakan da zinariya, ku kuma yi musu ƙawanen zinariya inda za a sa sandunan. Za ku dalaye sanduna kuma da zinariya.

30. Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.

31. “Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa.

32. Ku rataye shi a bisa dirkoki huɗu nan itacen ƙirya waɗanda aka dalaye da zinariya, da maratayansu na zinariya waɗanda aka sa cikin kwasfa huɗu na azurfa.

33. Za ku sa labulen a ƙarƙashin maɗauran, sa'an nan ku shigar da akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba tsakanin Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki.

34. Ku sa murfin a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki.

35. Sai ku sa teburin a gaban labulen wajen arewa, ku kuma sa alkukin a kudancin alfarwar daura da teburin.

36. Haka nan kuma za ku yi wa ƙofar alfarwa makari da lallausan zaren lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi, aikin mai gwaninta.

Karanta cikakken babi Fit 26