Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 26:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida.

23. Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa.

24. Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwan nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu.

25. Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu.

26. “Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya.

27. Biyar kuma domin katakai na wancan gefe. Har yanzu kuma biyar domin katakai na gefen yamma.

28. Sandan da yake tsakiyar katakan zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe.

29. Za ku dalaye katakan da zinariya, ku kuma yi musu ƙawanen zinariya inda za a sa sandunan. Za ku dalaye sanduna kuma da zinariya.

30. Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.

31. “Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa.

Karanta cikakken babi Fit 26