Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 26:15-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye.

16. Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi.

17. Za a fiƙe kan kowane katako. Haka za ku yi da dukan katakan.

18. Za ku shirya katakan alfarwa kamar haka, katakai ashirin wajen gefen kudu.

19. Ku kuma yi kwasfa arba'in da azurfa da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin kwasfa.

20. Za ku kuma kafa katakai ashirin wajen gefen arewa na alfarwar.

21. Haka kuma za ku yi kwasfa arba'in da azurfa dominsu. Kwasfa biyu domin kowane katako.

22. A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida.

23. Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa.

24. Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwan nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu.

25. Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu.

26. “Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya.

Karanta cikakken babi Fit 26