Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 26:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya.

12. Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar.

13. Kamu ɗayan da ya ragu a kowane gefe na tsawon, sai a bar shi yana reto a kowane gefe domin ya rufe alfarwar.

14. Za ku yi abin rufe alfarwa da fatun raguna da aka rina ja, za ku kuma yi wani abin rufewa da fatun da aka jeme.

15. “Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye.

16. Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi.

17. Za a fiƙe kan kowane katako. Haka za ku yi da dukan katakan.

18. Za ku shirya katakan alfarwa kamar haka, katakai ashirin wajen gefen kudu.

19. Ku kuma yi kwasfa arba'in da azurfa da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin kwasfa.

20. Za ku kuma kafa katakai ashirin wajen gefen arewa na alfarwar.

21. Haka kuma za ku yi kwasfa arba'in da azurfa dominsu. Kwasfa biyu domin kowane katako.

22. A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida.

23. Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa.

Karanta cikakken babi Fit 26