Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 25:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin.

19. Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin.

20. Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

21. Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka.

22. A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”

23. “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

24. Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

25. Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

26. Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin.

27. Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin.

28. Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin.

29. Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha.

Karanta cikakken babi Fit 25