Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 25:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi.

11. Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya.

12. Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon.

13. Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.

14. Ku sa sandunan a kafar kowace ƙawanya da take gyaffan akwatin saboda ɗaukarsa.

15. Za a bar sandunan cikin ƙawanen akwatin, kada a zare su.

16. A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin.

17. “Za ku yi wa akwatin murfi da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

18. Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin.

19. Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin.

20. Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

Karanta cikakken babi Fit 25