Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 23:2-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.

3. Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari'a.

4. “Idan wani ya iske san maƙiyinsa ko jakinsa ya ɓace, sai ya komar masa da shi.

5. Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa.

6. “Kada ku rasa yin adalci ga matalauci a wurin shari'a.

7. Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi da kuma adali, gama ba zan baratar da mugu ba.

8. Kada ku ci hanci, gama cin hanci yakan makantar da masu mulki, yakan kuma karkatar da manufar masu gaskiya.

9. “Kada ku wulakanta baƙo, kun dai san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.”

10. “Za ku nomi gonakinku shekara shida, kuna tattara amfaninsu.

11. Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun.

12. “Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake.

13. Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”

Karanta cikakken babi Fit 23