Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 23:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Za ku nomi gonakinku shekara shida, kuna tattara amfaninsu.

11. Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun.

12. “Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baĆ™inku su wartsake.

Karanta cikakken babi Fit 23