Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 23:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada wani ya haɗa baki da mugu ya zama munafukin mashaidi.

2. Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.

3. Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari'a.

4. “Idan wani ya iske san maƙiyinsa ko jakinsa ya ɓace, sai ya komar masa da shi.

5. Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa.

6. “Kada ku rasa yin adalci ga matalauci a wurin shari'a.

7. Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi da kuma adali, gama ba zan baratar da mugu ba.

8. Kada ku ci hanci, gama cin hanci yakan makantar da masu mulki, yakan kuma karkatar da manufar masu gaskiya.

9. “Kada ku wulakanta baƙo, kun dai san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.”

10. “Za ku nomi gonakinku shekara shida, kuna tattara amfaninsu.

11. Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun.

12. “Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake.

13. Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”

14. “Sau uku a shekara za ku yi mini idi.

15. Wajibi ne ku yi idin abinci marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Za ku ci abinci marar yisti kwana bakwai lokacin da aka ayyana a watan Abib, gama a wannan wata ne kuka fito daga Masar. Kada wani ya zo wurina hannu wofi.

16. Ku kuma yi idin nunan fari na amfanin gonakinku da kaka. Sa'an nan kuma za ku yi idin gama tattara amfanin gonakinku a ƙarshen shekara.

17. Sau uku a shekara mazaje za su gabatar da kansu a gaban Ubangiji.

18. “Kada ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti. Kada kuma ku ajiye kitsen abin da aka yanka a lokacin idina, ya kwana.

Karanta cikakken babi Fit 23