Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 21:27-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Idan ya fangare haƙorin bawansa ko na baiwarsa, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon haƙorin.”

28. “Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta.

29. Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi.

30. Idan an yanka masa diyya, sai ya biya iyakar abin da aka yanka masa don ya fanshi ransa.

31. Haka kuma za a yi idan san ya kashe ɗan wani ko 'yar wani.

32. Idan san ya kashe bawa ko baiwa, sai mai san ya biya wa ubangijin bawan, ko baiwar, shekel talatin a kuma jajjefi san.

33. “Idan mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai rufe ba, in sa ko jaki ya fāɗa ciki,

34. mai ramin zai biya mai san ko mai jakin, mushen ya zama nasa.

35. Idan san wani ya yi wa na wani rauni har ya mutu, sai ya sayar da san da yake da rai a raba kuɗin. Haka kuma za su raba mushen.

36. Amma idan dā ma an sani san mafaɗaci ne, mai san kuwa bai kula da shi ba, sai ya biya, wato ya ba da sa a maimakon mushen. Mushen kuwa zai zama nasa.”

Karanta cikakken babi Fit 21