Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 21:23-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma in wani lahani ya auku, to, sai a hukunta rai a maimakon rai,

24. ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa,

25. ƙuna a maimakon ƙuna, rauni a maimakon rauni, ƙujewa a maimakon ƙujewa.

26. “Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya lalace, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon idon.

27. Idan ya fangare haƙorin bawansa ko na baiwarsa, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon haƙorin.”

28. “Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta.

29. Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi.

Karanta cikakken babi Fit 21