Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 21:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓāta masa, ya kuma lura da shi har ya warke sarai.

20. “In mutum ya dūki bawansa ko baiwarsa da sanda har ya mutu a hannunsa, lalle ne a hukunta shi.

21. Amma idan bawan ya rayu kwana ɗaya ko biyu, to, kada a hukunta shi, gama bawan dukiyarsa ne.

22. “Idan mutum biyu na faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka zai biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara.

23. Amma in wani lahani ya auku, to, sai a hukunta rai a maimakon rai,

24. ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa,

25. ƙuna a maimakon ƙuna, rauni a maimakon rauni, ƙujewa a maimakon ƙujewa.

26. “Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya lalace, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon idon.

27. Idan ya fangare haƙorin bawansa ko na baiwarsa, sai ya 'yanta bawan ko baiwar a maimakon haƙorin.”

Karanta cikakken babi Fit 21