Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 21:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Waɗannan su ne ka'idodin da za a ba Isra'ilawa.

2. Idan ka sayi bawa Ba'ibrane, zai yi bauta shekara shida, a shekara ta bakwai kuwa, a 'yantar da shi kyauta.

3. Idan yana shi kaɗai aka saye shi, sai ya fita shi kaɗai, idan kuwa yana da aure sa'ad da aka saye shi, sai matarsa ta fita tare da shi.

4. Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa 'ya'ya mata ko maza, to, matar da 'ya'yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita.

5. Amma idan hakika bawa ya hurta ya ce, yana ƙaunar ubangijinsa, da matarsa, da 'ya'yansa, ba ya son 'yancin,

6. to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa'an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa.

7. “Idan mutum ya sayar da 'yarsa kamar baiwa, ba za a 'yanta ta kamar bawa ba.

8. Idan ba ta gamshi maigidanta wanda ya maishe ta kamar ɗaya daga cikin matansa ba, sai ya yarda a fanshe ta. Amma ba shi da iko ya sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.

Karanta cikakken babi Fit 21