Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 20:4-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.

5. Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.

6. Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararrakin da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.

7. “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.

8. “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki.

9. Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida,

10. amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku.

11. Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.

12. “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

13. “Kada ka yi kisankai.

14. “Kada ka yi zina.

15. “Kada ka yi sata.

16. “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.

Karanta cikakken babi Fit 20