Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 20:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

13. “Kada ka yi kisankai.

14. “Kada ka yi zina.

15. “Kada ka yi sata.

16. “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.

17. “Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”

18. Da jama'a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa.

19. Suka ce wa Musa, “Kai, ka yi magana da mu, za mu ji, amma kada Allah ya yi magana da mu don kada mu mutu.”

20. Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo ne don ya jarraba ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”

21. Sai jama'a suka tsattsaya nesa, Musa kuwa ya matsa kusa da girgije mai duhu inda Allah yake.

22. Ubangiji ya ce wa Musa, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku da kanku kun ji na yi magana da ku daga sama.

23. Banda ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa da na zinariya.

24. Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama, da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka.

25. Idan kuwa za ku gina mini bagade na dutse, kada ku gina mini da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama idan guduma ta taɓa duwatsun sun haramtu.

26. Kada ku yi wa bagadena matakai domin kada tsiraicinku ya bayyana a bisansu sa'ad da kuke hawansu.”’

Karanta cikakken babi Fit 20