Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 15:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,“Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.

2. Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,Shi ne wanda ya cece ni.Wannan ne Allahna, zan yabe shi,Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

3. Ubangiji mayaƙi ne,Yahweh ne sunansa.

4. “Karusan Fir'auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar,Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.

5. Rigyawa ta rufe su,Suka nutse cikin zurfi kamar dutse.

Karanta cikakken babi Fit 15